Gwamnatin tarayya ta Najeriya ta dauki sabon mataki da ke saukaka shigar dalibai kwalejojin ilimi, inda ta cire wajabcin rubuta jarrabawar UTME ga masu neman karatun NCE.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya bayyana wannan sauyi a birnin Abuja yayin taron tsara manufofin shigar dalibai zuwa jami’o’i da sauran manyan makarantu na shekarar 2026.
Ya bayyana cewa daga shekara mai zuwa, duk dalibi da ya samu akalla darussa hudu da suka hada da kredit a matakin da ake bukata, zai iya shiga shirin NCE ba tare da rubuta UTME ba.
Sai dai ya jaddada cewa dole ne irin wadannan dalibai su yi rajista da hukumar JAMB domin tantance takardunsu kafin a ba su gurbin karatu ta tsarin CAPS.
A cewarsa, wannan sabon tsari na da nufin fadada damar samun ilimi, rage cunkoso da matsin lamba kan jarrabawar UTME, tare da karfafa sha’awa ga koyarwa da kuma fannin noma.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa ta fadada irin wannan sassauci ga masu neman shiga manyan difloma a wasu fannonin noma da ba na fasaha ba, domin inganta ilimi da kwarewa a kasar.
