FIFA ta sauya dokar katin gargadi a kofin Duniya na 2026

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) ta sanar da sabuwar dokar katin gargadi (yellow card) gabanin Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, inda ta bai wa ‘yan wasa rangwame kan katunan da suka tara a matakin rukuni.

Sabuwar dokar ta tanadi cewa katin gargadi da ‘yan wasa suka tara a matakin rukuni ba zai haifar da dakatarwa a matakin knockout ba, idan aka wuce matakin rukuni na gasar.

An amince da wannan sauyi ne a taron majalisar FIFA da aka gudanar a ranar Talata, sannan aka bayyana shi a hukumance daga baya.

FIFA ta ce sauyin ya zama dole saboda fadada gasar zuwa ƙasashe 48, da kuma bukatar tabbatar da cewa ‘yan wasa masu muhimmanci ba sa rasa manyan wasannin knockout saboda katunan gargadi.

A cewar FIFA, za a soke katin gargadi guda ɗaya da aka tara bayan matakin rukuni, sannan kuma za a sake yin hakan bayan wasan kwata fainal, domin rage yiwuwar dakatar da ‘yan wasa a manyan matakai.

FIFA ta fara amfani da tsarin rangwame na katin gargadi bayan kwata fainal tun Gasar 2010 a Afirka ta Kudu, bayan shahararren abin da ya faru a 2002 inda Michael Ballack ya rasa wasan karshe na gasar.

Gasar 2026 FIFA World Cup za a gudanar a ƙasashen United States, Mexico da Canada daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version