Farashin mai a kasuwannin duniya ya fara nuna ɗan ƙaruwa duk da rashin daidaito a kasuwa, yayin da ake ci gaba da jiran sakamakon tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran.
Rahotanni sun nuna cewa farashin man Brent ya kai kusan dala $109 a kowace ganga, yayin da na WTI ya zarce dala $112. Wannan tashin farashi na zuwa ne bayan matsalolin safarar mai da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya.
Babban abin da ke jawo damuwa shi ne halin da ake ciki a mashigar Strait of Hormuz, wadda ke da muhimmanci wajen jigilar mai daga kasashe kamar Saudi Arabia, Iran da UAE. Rufe mashigar ya janyo tangarda ga kasuwannin duniya, lamarin da ya tilasta wasu kasashe neman madadin mai daga wasu wurare.
Duk da cewa an gabatar da tsarin tsagaita wuta, Iran ta nuna kin bude mashigar nan take, wanda halan ke kara jefa kasuwar mai cikin rudani. Masana sun ce idan rikicin ya ci gaba, farashin mai na iya kara tashi fiye da yadda ake gani yanzu.
