Farashin Mai Ya Fadi A Kasuwannin Duniya

Farashin danyen mai ya fadi a kasuwannin duniya yayin da hannayen jari suka tashi, sakamakon rahotannin da ke nuna cewa United States da Iran na gab da cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikici.

Rahotanni sun nuna cewa farashin mai na Brent ya sauka zuwa ƙasa da dala 100 kan kowace ganga.

Farashin danyen mai ya kasance cikin tashin gwauron zabi tun bayan fara rikicin da ya shafi Amurka da Israel kan Iran, lamarin da ya janyo takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz.

A gefe guda kuma, kamfanonin jiragen sama sun rage kusan tashin jirage 13,000 a sassa daban-daban na duniya a cikin watanni, sakamakon hauhawar farashin man jirgin sama.

Masu sharhi sun ce rikicin ya shafi kusan fasinjoji miliyan biyu a duniya, yayin da ake ci gaba da fargabar tasirin lamarin kan tattalin arzikin duniya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version