El-Rufai Ya Samu Belin Naira Miliyan Dari A Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya samu beli daga wata babbar kotu da ke Abuja bayan an gurfanar da shi kan zargin da ya shafi barazana ga tsaron kasa. Alkalin kotun, Mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta bayyana cewa an bayar da belin ne kan kudi Naira miliya 100 tare da wasu sharudda da dole a cika kafin a sake shi.

Kotun ta kuma gindaya cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance mazaunin yankunan Maitama   ko Asokoro da ke Abuja. Wannan sharadi na daga cikin matakan da kotun ta dauka domin tabbatar da cewa za a ci gaba da bin shari’ar yadda ya kamata.

Lauyoyin El-Rufai sun nuna gamsuwa da hukuncin bayar da belin, yayin da ake sa ran za a ci gaba da sauraron karar a kwanaki masu zuwa. Shari’ar dai ta jawo hankalin jama’a da dama saboda matsayin El-Rufai a siyasar Najeriya da kuma irin tasirin da yake da shi a fagen siyasa.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version