EFCC Ta Ayyana Neman Sadiya Umar Farouq

Economic and Financial Crimes Commission ta ayyana neman tsohuwar ministar jin kai ta Najeriya, Sadiya Umar Farouq, ruwa a jallo bisa wasu zarge-zargen da ake yi mata.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa, EFCC ta ce ana neman tsohuwar ministar ne kan zargin haɗa baki wajen aikata laifuka, amfani da ofishi ba bisa ƙa’ida ba da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati.

Hukumar ta kuma buƙaci al’umma da su kai rahoto ga jami’anta idan suka ga ko suka samu bayanin inda tsohuwar ministar take domin sauƙaƙa cafke ta.

Karanta cikakken labarin: EFCC: Akwai Fastoci da Limamai a Tsare kan Zargin Damfara

Sadiya Umar Farouq ta riƙe muƙamin ministar jin ƙai a lokacin gwamnatin marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version