Shugaban Economic and Financial Crimes Commission, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa akwai wasu shugabannin addini da suka haɗa da Fastoci da Limamai da ke tsare a hannun hukumar bisa zargin aikata damfara da wasu laifukan kuɗi.
Ya ce wasu daga cikinsu ma tuni kotu ta same su da laifi tare da yanke musu hukunci.
Olukoyede ya bayyana hakan ne yayin bikin bayar da tallafin kasuwanci na gidauniyar Jerry Eze.
A cewarsa, cin hanci da rashawa ba ya tsaya ga ƴan siyasa ko kamfanoni kaɗai, domin har cibiyoyin addini ma na fuskantar bincike dangane da zargin almundahana da rashin gaskiya.
“Yanzu haka akwai da dama daga cikinsu a cibiyar tsarewar EFCC, yayin da wasu kuma aka riga aka yanke musu hukunci saboda damfara,” in ji shi.
Ya jaddada cewa rashin ɗa’a ko cin amana laifin mutum ne kai tsaye, ba wai addini ba, yana mai cewa duka majami’u da masallatai na iya fuskantar matsalolin amfani da iko ba daidai ba.
Shugaban EFCC ya ce ƙwarewar hukumar ta nuna cewa gaskiya da riƙon amana suna cikin halayen mutum ne, ba wai mukami ko matsayi na addini ba.
Olukoyede ya kuma tunatar da jama’a cewa dokar Companies and Allied Matters Act (CAMA) ta bai wa gwamnati damar shiga harkokin ƙungiyoyi da cibiyoyin addini idan akwai zargin damfara, rashin gaskiya ko almundahana.
Haka kuma ya bayyana cewa EFCC ta taɓa gudanar da bincike kan Fasto Jerry Eze bayan samun bayanan sirri da suka nuna akwai kuɗaɗen ƙasashen waje masu yawa da ke shiga asusunsa daga ƙasashe daban-daban.
Karanta: Har Yanzu Nasir El-Rufai na Hannun EFCC
Sai dai ya ce bayan binciken da ya ɗauki watanni shida, hukumar ba ta samu wata shaida ta halasta zargin wanke kuɗi ko wata badakala a kansa ba.
A ƙarshe, Olukoyede ya ce ya kamata EFCC ba kawai a riƙa danganta ta da masu laifi ba, har ma da mutanen kirki masu gaskiya da riƙon amana.
