DSS Ta Kara Cafke El-Rufai Bayan Samun Belinsa

Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun sake kama tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, jim kadan bayan wata babbar kotu da ke Abuja ta amince da bayar da belinsa kan wasu zarge-zarge da ake yi masa.

Lamarin ya jawo ceceku ce a tsakanin magoya bayansa da wasu yan siyasa, yayin da ake jiran karin bayani daga hukumomin tsaro dangane da dalilin sake cafke shi bayan samun beli daga kotu.

Rahotanni sun bayyana cewa an dauke shi ne daga harabar kotun bayan kammala shari’ar ranar.

Tun farko, kotun ta bayar da belinsa kan kudi Naira miliyan 100 tare da sharadin samun wanda zai tsaya masa daga yankunan Maitama ko Asokoro a Abuja.

Sai dai bayan fitowarsa daga kotun, jami’an DSS suka sake tsare shi domin ci gaba da bincike kan zarge-zargen da ake yi masa.

Lamarin ya jawo ceceku ce a tsakanin magoya bayansa da wasu yan siyasa, yayin da ake jiran karin bayani daga hukumomin tsaro dangane da dalilin sake cafke shi bayan samun beli daga kotu.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version