Dan wasan Ghana, Dominick Frimpong ya rasu

Dan wasan kungiyar Berekum Chelsea, Dominick Frimpong, ya rasu bayan wani harin ƴan fashi da aka kai wa motar bas din da ke ɗauke da tawagarsu bayan sun kammala wasa da FC Samartex a gasar Premier ta Ghana.

Matashin ɗan wasan mai shekara 20 ya samu munanan raunuka sakamakon harbin bindiga lokacin da aka buɗe wa tawagar tasu wuta.

Frimpong, wanda ɗan wasan Aduana FC ne, yana taka leda a Berekum Chelsea ne a matsayin aro. Ya buga wasanni 13 a bana tare da zura ƙwallaye biyu.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version