Daga Aysha Balkisu Umar : Yawancin ‘yam matan da suke so su auri mai mata suna gudun saurayi ne sabo da suna gudun wahala. Yawancin samari ba su da kudi, yanzu suke fafutukar gina rayuwar, da kokarin fuskantar inda ta dosa, rashin gidan kai na gani na fada, rashin mota, kokarin tallafawa iyaye da kanne, malejin rayuwa, in aikin gwamnati ake yi yanzu aka fara, sai an kai a kalla shekara 15 zuwa 20 kafin a fara daukar wani albashi mai tsoka, ko kafin a kira shi ya amsa, to ga wanda ma yake da aikin kenan. Idan yana daukar albashin dubu dari, haka zaku raba tsakanin biyan kudin haya, hospital bills dinki (dan ma Allah ya taimakeki kin zo a zamanin NHIS) ciyar da ke da iyayensa, kudin makarantar kannensa, maintenance na yau da kullum da sauransu. Ga uwa uba rashin experience na auren, zafin kai irin na matashi, dokoki kala-kala, saurin fishi da hidindimu da su kai masa yawa, ga rashin gogewa wajen mu’amala da mace da halayenta, SABO DA SHI AURE, KOYONSA AKE!
Wasu ‘yammatan kuma da yawa sun kai lokacin da sun fi karfin saurayi, samari ba za su aure su ba, watakila shekaru da budewar ido su jawo mata haka, sannan su ma za su fi son wanda ba zai matsa musu ko takura musu ba, dan haka gara mai mata sabo da su cigaba da rayuwarsu yadda suke so kuma suka tsara, ba sa ido da dokoki. Wasu da yawa inda suke aiki ma sai a tara samari dari da basa daukar rabin albashin da take dauka, to suma sun san su ce dole-dole sai saurayi sun yaudari kan su. Dan daidai ruwa daidai tsaki.
Wadannan dalilan da yawa da ma wasu, musamman na farko sun sa ‘yammata yanzu Allah-Allah suke su hango wani senior civil servant din, ko wani matashin mai business ko wanda dai ya fara kama kasa a wajen aikinsa su yi alaragab da shi. Sabo da suna gudun waccen wahalar ta auren saurayi mai fafutukar gina rayuwa. Ko banza za ai mata gida da mota da lefe na gani na fada sannan a kaita asibiti mai kyau idan ta tashi haihuwa. Amma fa da yawa ba sa iya jure halin mai mata, so suke sai ya bar iyalinsa ya kama hira da ke. Hajiya, kin manta matar data aure shi a irin waccen wahalar da kike gudu a yanzu? Baki san cewa komai nasa a yanzu nata ne ba, bare wata aba waya da har kike so sai an mata iyaka da wayar mijinta? Duk wata kwalliya ta duniyar nan tai masa, duk wata tarairaya da girki mai dadi an dafa masa ya ci kafin naki, duk wata shagwaba ba wadda ba ai masa ba, duk wani d’oki da farinciki na ‘yayan da zaki haifa an haifa masa. Babu wata hanya da zaki tallafa wajen gina rayuwarsa sabo da rayuwarsa ta gama ginuwa da wata da bata tsoraci talauci ba. Ke kawai kin zo ki sha romon demokradiyya ne, dan haka sai ki bi a hankali.
Yana da wahala a yanzu ki samu mijin da “he is not own by his wife” dan haka ke second choice ce har abada, kuma kin sani. Karin aure ba laifi ba ne, akwai shekarun da in suka ja, namiji kan bukaci wata macen ba wai wata abokiyar rayuwar ba dan already yana da ita, wadda suka koyi aure kuma suka iya shi tare.
Allah ya bawa masu kyakkyawar niyya game da aure abokan rayuwa na gari.