Daga karshe jam’iyyar APC ta tabbatar da nasarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam, Yusuf Gagdi, bayan kammala zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar Plateau.
Wannan mataki ya kawo karshen ce-ce-ku-cen da suka biyo bayan sakamakon zaben cikin gida na jam’iyyar.
Rahotanni sun bayyana cewa shugabannin APC a jihar sun amince da sakamakon zaben bayan tantance kuri’u da kuma duba yadda tsarin zaben ya gudana.
Magoya bayan Gagdi sun yi murna tare da bayyana cewa nasarar tasa ta nuna irin goyon bayan da yake samu daga al’ummar mazabarsa.
A nasa bangaren, Yusuf Gagdi ya gode wa shugabannin jam’iyya da magoya bayansa bisa amincewar da suka nuna masa, yana mai alƙawarin ci gaba da wakiltar jama’a da gaskiya da jajircewa idan aka sake zabensa a babban zaben shekarar 2027.
