Jami’an Hukumar Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC) sun gudanar da bincike a gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El‑Rufai, da ke Abuja a ranar Alhamis.
Mai ba tsohon gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce jami’an sun isa gidan tare da fara binciken sassa daban daban nan take.
Sai dai lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya soki matakin, yana mai cewa binciken da aka gudanar ba bisa ka’ida ba ne, kuma ya saba da dokoki da hakkokin dan Adam.
A baya dai, a ranar Laraba, ICPC ta sanar da cewa tsohon gwamnan yana hannunta dangane da wani bincike da take yi, amma ba ta bayyana cikakken bayani kan zarge-zargen da ake masa ba.
