Jam’iyyar ADC, wadda ke cikin haɗakar ƴan hamayya a Najeriya, ta ayyana ranar 12 ga watan Mayu mai zuwa domin rantsar da sabbin shugabanninta a faɗin ƙasar.
A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na ɓangaren David Mark, Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta taya murna ga mambobinta bisa gudanar da tarukan jihohi na zaɓen shugabanni cikin lumana da kwanciyar hankali.
Sanarwar ta ce wannan mataki yana nuna ƙudirin jam’iyyar na bin tafarkin dimokraɗiyya tare da mutunta doka da oda.
Haka kuma, jam’iyyar ta buƙaci sabbin shugabannin jihohi da aka zaɓa su yi aiki tare da uwar jam’iyya ƙarƙashin jagorancin David Mark, domin ƙarfafa jam’iyyar a duk faɗin Najeriya.
Karanta: ADC Ta Zargi INEC da Shirya Mata Tarko
A baya dai, shugaban hukumar zaɓen jam’iyyar, Farfesa Joash Amupitan, ya gargaɗi ADC da kada ta gudanar da irin waɗannan taruka, yana mai cewa hakan na iya saɓa da umarnin kotu da ya rusa tsohon shugabancin jam’iyyar.
