A Litinin da ta gabata, mun tsaya daidai inda aka ce: Wannan bayani na matarsa, maimakon ya huce masa zuciya sai ya ji wani bak’in ciki ya tokare masa k’irji. Wannan ya sanya ya rufe ido, ya ci gaba da magana. “Wane hak’uri, wane irin hak’uri zan yi da abin takaici? Bayan kun maida ni dattijon banza, na zama abin kwatance a gari. Ki duba fa, duk k’awayenta sun dad’e da tsufa a gidajen aurensu, ita kuwa sai iya karatun aku da ziyarar k’awaye. To, wallahi ba zan ci gaba da lamuntar wannan wulak’ancin ba. Ya zama dole a yi wa tufk’a hanci, a san wacce za a yi. Idan ba haka ba kuwa ni da ku!”
Yau kuma ga ci gaba:
Wurin ya yi tsit kamar an yi mutuwa. Zinatu ta yi kasak’e, ta fara kyarma kamar wacce ruwan sama ya ba kashi. Ji take kamar zazzab’i zai saukar mata. Mahaifiyarta kuwa, ta ma rasa abin cewa. Malam Nakande ya d’auki butar sahani da ke kusa da hannunsa na dama, ya guntsi ruwa, ya kurkure baki ya furzar k’asa sannan ya juya fuskarsa b’angaren Zinatu.
Malam Nakande ya ce: “To, ke kuma na juyo kanki, me ake ciki? Kwanaki kin ce mani jarabawarku ta fito, kin amso takardar sakamakon? Kuma ina maganar wannan yaron da na gani rannan kuna zance a k’ofar gida?”
A lokaci guda ya fesa mata wad’annan mabambantan tambayoyi. Dalili ke nan ya sanya har ta rud’e, duk kuwa da cewa ta dad’e da sabawa da kurarinsa. Kai, ita dai gani take kamar ba ta dace da iyaye ba. A ce kullum sai fad’a! Tana mamakin kasancewarta ’yar auta amma ake azazzalarta haka. Ta ji fa an ce ’yar auta shalele ce ga iyaye amma ita ga shi an mayar da ita kamar ’yar fari! ‘Dan tunanin nan da ta yi na dak’ik’a uku, shi ya ba ta k’arfin halin ba shi amsa da cewa:
“Baba, in Allah Ya kai mu gobe, ina son zuwa makaranta, domin in amso sakamakon jarabawar. Kuma idan na amso, ina son ka ba ni izini in d’an fara aiki na wucin-gadi kafin in yi aure; maganin zaman banza.”
Da kishingid’e yake bisa gorar hannunsa na dama amma kalaman d’iyarsa suka sanya ya yi zumbur ya mik’e zaune. Ya darkako mata k’ulu-k’ulun idanuwansa cike da mamaki. Tabawa kuwa ta yi kasak’e, ta ma rasa abin cewa.
“Aiki, aiki, ai me?”
Cikin mamaki da fushi da alamar kamar zai kai mata duka yake magana.
“Haba, ashe wata sabuwar lalatar kuka shirya mani? Lallai fa! Ta nan kuma kuka b’ullo mani? To, wallahi k’aryarku ta sha k’arya! Ashe maganar da ake gaya mani gaskiya ce? An ce da zarar mace ta bud’e ido da karatun boko, gani take ta samu sabon ’yanci, tana ganin d’aya take da maza. To, ga gaskiyar lamarin ta fito a gidana.”
Ya d’an dakata, a yayin da ya juyo fuskarsa wajen Tabawa; ya d’aga manuninsa na hannun dama, yana ishara zuwa gare ta.
“To, Tabawa kun gama k’ure ni, don haka ga kashedina nan na k’arshe. Na ba ku daga nan zuwa mako biyu masu zuwa, ya zama dole ta fito da miji ko kuma ku zab’i na zab’e. Idan ba miji, zan had’a ta aure da duk wanda na ga dama, ko kuma ta sake uba kuma ta sake gida; ba dai gidana ba. Ku tashi ku ba ni wuri!”
Yana gama fad’in haka sai ya kama tari, dattin goro ne ya shak’e shi. Ya fizgo buta, ya tsotsi ruwa. Ita kuwa Tabawa da d’iyarta suka tashi sumui-sumui, suka kama hanyar d’aki.
Saboda takaicin abin da ya faru, Tabawa sai ta fasa zuwa barkar haihuwar da ta shirya zuwa. Sawun giwa ya take na rak’umi! Tun zamanta da Malam Nakande a matsayin miji da mata, yau tsawon shekaru arba’in da uku ke nan amma ba ta tab’a ganin zafin b’acin ransa irin na yau ba. Dalili ke nan ya sanya ta ma rasa matakin da za ta d’auka kan wannan al’amari. Ta Hausawa da suka ce, zomo ba ya fushi da makashinsa sai maratayinsa. Kan haka, da suka koma d’aki sai ta hau Zinatu da fad’a gami da zagi. Ta inda ta shiga, ba ta nan take fita ba.
Zinatu kuwa bak’in ciki ya cika mata ciki fal, ta ma rasa abin da ke mata dad’i. Koda ta kishingid’a bisa katifarta, babu abin da take yi sai tunani. Ta k’ulla wannan, ta kwance wancan. A kan haka ta d’aga kai jikin bango, ta kalli agogo; k’arfe biyu da rabi daidai na dare amma duk da haka idanuwanta sun k’ek’ashe, barci ya k’aurace masu. Ba ta san lokacin da k’walla ta cika mata idanu ba.
Ba ita ta samu barci ba sai da ta yi alwalla, ta dubi gabas ta yi Sallar nafila raka’a biyu, sannan ta yi wutiri raka’a d’aya, ta rok’i Allah Ya sauk’ak’a mata al’amarinta. Daga nan ta dawo bisa shimfid’arta, ta nemi barci amma ya faskara.
A kan haka ta samu kanta cikin wani tunanin. Ta tuno wata rana da malaminsu na Islamiyya ya tab’a ba su shawara kan irin wannan yanayi. Ya ce masu duk lokacin da mutum ya samu kansa cikin k’ik’i-k’ak’a kuma ya rasa tudun dafawa, to babu abin da ya kamata mutum ya yi sai addu’a.
“Addu’a ce babbar garkuwar d’an Adam. Addu’a na maganin kowane irin bala’i kuma tana tare da fa’idoji masu d’inbin yawa. Babu wani lokaci mafi tasirin amsar addu’a kamar tsakiyar dare…”
Wad’annan kalamai take ji suna k’wank’wasa mata k’wak’walwa. Jinsu take yi garau, kamar ma yanzu ne yake fad’arsu. Nan da nan ta samu kanta cikin addu’a. Ta karanta Fatiha k’afa uku, Ayatul Kursiyyu k’afa uku; daga nan kuma ta lalubo aya ta goma ta cikin Suratul Kahfi: “Rabbana atina milladunka rahmatan wa hayyilana min amrina rashada.”
K’afa uku ta biya na wannan muhimmiyar addu’a, domin kuwa tana sane da labarin addu’ar, kamar yadda malamin nasu ya shaida masu. Ta tuno yadda ya gaya masu cewa, salihan bayin nan da ake kira Mutanen Kogo, su ne suka karanta ta, a lokacin da suka b’oye cikin duhun kogo, suka nemi Allah Ya yi masu agaji da rahamarSa kuma Ya sauk’ak’a masu al’amarinsu. Yalai kuwa, Allah Ya biya masu buk’atunsu, Ya kare su daga cutarwar masu mulkinsu na lokacin, sannan Ya sanya masu aminci mai yawa har suka samu tsira.
Zinatu ba ta tsaya kan wannan addu’a ba, sai da ta rufe da K’ula’uzai k’afa uku-uku sannan ta samu barci. Ba ta farka ba sai da sanyin safiya.
ZA A CI GABA RANAR LITININ, IN SHA ALLAH!
© #Bashir_Yahuza_Malumfashi
Laraba 27-06-1442 (Hijriyya)