Zinatu Matar Gwamna 2 – Babi Na 1

A makon jiya mun tsaya daidai inda aka ce: “Duk da cewa ta kammala wanke-wanken kwanonin, sai ta samu kanta zaune a kujera, ta kasa tashi daga wurin. Wannan abin bak’in ciki da ke dabaibaye ta, ya saka ta cikin k’unduttu; dalili ke nan ya sanya ta ci gaba da tunano hirar da suka yi jiya da k’awarta. K’awarta ce Balaraba ta k’ara tabbatar mata da cewa, lallai ita da samun sauk’in irin wad’annan tsegunguma sai ta yi aure ko kuma wani sanadi ya zo, yadda za ta rabu da iyayenta.” Yau kuma ga ci gaba:

“Ina son ki gane yanayin al’adunmu da na addininmu.” Inji Balaraba. “A k’asar Hausa, saboda tasirin addini, yarinya da ta fara girma, ta zama abin tashin hankali ke nan ga iyayenta. Ba za su sake samun kwanciyar hankali ba sai sun ga ta yi aure. Idan ba haka ba kuwa, to, ba za su guje wa maganganu da tsegunguman mak’wafta ba. Idan an yi rashin sa’a kuma sai ki ji ana yi mata yarfe da cewa, ta yi kwantai.”

“To, amma ai ya kamata mu gane cewa duniya ta canza; da da yanzu ba d’aya ba ne. A zamanin da, kamar yadda muka karanta a tarihi, babu yawan al’umma kamar yanzu, babu talauci da kwad’ayin neman duniya kamar yanzu. Haka kuma, babu ilimin zamani, inda mata da maza za su samu wayewa. To, tun da yanzu duk wad’annan al’amura sun samu canji, me zai hana mu canza mu ma?” Zinatu na k’arin bayani ga k’awarta. Suna tafiya ne bisa titi da maraice. Ga alama, sun dawo daga kasuwar ’Yar Kutungu ne; suna dawowa zuwa gida.
Balaraba ta tauna cingam da k’arfi, ta hura shi bisa leb’b’anta, ta yi balo da shi, sannan ta maida shi cikin baki.

“Kash! Zinatu, kin mance da wani abu d’aya. Da kike cewa duniya ta canza, wane ne ya canza? Ina son ki gane cewa, mu matasa da k’ananan yara, ’yan zamani; mu ne muka canza, amma su baba da inna da kakanninmu fa? Sun canza ne? Don haka, dole ne za mu ci gaba da tafiya haka, suna tafiya, ana canzawa a hankali; har nan gaba yanayinmu da al’adunmu sai su canza.”
“Na yarda da wannan bayanin naki, amma me iyayenmu ke gudu, da suke matsa mana haka game da aure?” Zinatu ta ci gaba da magana, amma ba ta jira amsar k’awarta ba, sai ta ci gaba da bayaninta. “Ina ganin namiji ne ya kamata ya nemi yarinya da aure ko? To, idan bai nema ba fa? Ya kamata yarinya ta je wajen saurayi ne tana rok’onsa, cewa ya zo ya aure ta? Ai wannan zubar da mutunci ne kuma ya sab’a wa al’adar Malam Bahaushe. Ni kam gani nake kamar gajiya aka yi da ni a gidanmu, shi ya sa ake tsangwama ta, wai in yi aure. Duka yaushe na gama wannan makarantar? Ki tuna fa ko jarabawarmu ma ba ta ida fitowa ba.”
Balaraba ta tuntsure da dariya, har tana tuntub’e. Takalminta ne ya ci karo da wani bulo da ke gefen hanya. Ta yi tangal-tangal haka, kamar za ta fad’i. “Shegiya! Wallahi kin sanya ni dariya kan titi haka, kamar zautatta. Wai an gaji da ke, babu wanda ya gaji da ke. Su a ganin su, abin kunya ne d’iyarsu ta kai kamar ki ba ta samu miji ba. Kuma suna tsoron abin kunya, musamman kada wani shege ya d’irka maki ciki, ki haifar masu d’an rariya.”
“Haba, haba, don Allah ki bar wannan maganar. Ai ni ban ga d’a namijin da ya isa ya yi mani wannan sakarcin ba. Ki tuna fa ina da ilimi hagu da dama. Kin san dai na sauke Alk’ur’ani bara, ga shi ma har na fara hadda. Arba’una Hadis kuwa tuni na sauke shi, har ma na fara shiga manyan littattafan Fik’ihu. Ta b’angaren karatun zamani kuwa, ba sai na gaya maki ba, tun da aji d’aya muke; kwalin difiloma kawai muke jira. Don haka, duk illar zinace-zinace ba wacce ba mu sani ba. To, yaushe zan zubar da mutuncina har in yarda da wani mayaudari ya yaudare ni?”
Zinatu na gama wannan batu sai Balaraba ta amshe, ta ce: “Ni dai ina ganin mu bi a hankali da iyayenmu, mu lallab’a da su, mu rabu lafiya. Tun da dai mun yi karatun nan na zamani, sai mu k’ok’arta mu yi ta rok’on Allah Ya koro mana da mazajen aure. Mu yi aurenmu mu huta, alabashi idan muna d’akunan mazajenmu sai mu san hikimar da za mu shawo kansu, su bar mu mu ci gaba da neman ilimi ko kuma ma mu yi aiki ko sana’ar neman kud’i, don rufin asirin kanmu.” Da wannan zancen ne suka kawo inda za su rabu, kowace ta kama hanyar gidansu.
***
ZA A CI GABA RANAR LARABA, IN SHA ALLAH!
————————————–
© #Bashir_Yahuza_Malumfashi
Litinin 18-06-1442 (Hijriyya)
01-02-2021 (Miladiyya)
————————————-

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version