Zaune take bisa ’yar k’aramar kujerar mata. A gabanta, tsibin kwanukan abinci ne tare da tukwanen da ke dank’are da k’anzo, k’udaje na ta shawagi bisansu. Zinatu ta k’ura masu hajar mujiya kamar mai zullumin wanka. Ga dukkan alamu, hankalinta ba ya kan wannan tsibin kayan wanke-wanken da ke gabanta. Babu shakka akwai wani abu muhimmi da ya d’auke mata hankali kuma take tunaninsa.
“Saboda me za a matsa mani kan maganar aure, alhali ba kaina farau ba? Ko kuwa dai an gaji da ni ne a gidan nan?” Tunaninta ya gawurta, ya rikid’e daga na zuciya zuwa magana. Ta samu kanta cikin furta wasu kalamai ita kad’ai kamar zautatta. Ita kad’ai ke magana, babu kowa kusa da ita, in ban da wad’annan tsibin kwanoni da ke gabanta, suna jiran wankewa.
“…Ko kuwa dai ni ba d’iyar gidan nan ba ce, ko ba inna da baba ne suka haife ni ba?” Ta ci gaba da magana a fili.
“To, idan ba haka ba, yaushe za a maida ni kamar wata baiwa? Kullum ni ake tara wa duk wani aikin gida. Sannan ga shi an tsangwame ni da fad’a da tsegumi, wai na k’i yin aure; kamar so ake in kai kaina talla kasuwa!” Cikin alamar damuwa da b’acin rai take wad’annan kalamai.
“Ke sababba, ke za mu jira ko kuwa? Kin tasa kwanoni gaba kin k’i wankewa, ko kuwa ni kike jira in wanke maki?” Wannan magana mai kama da tsawa, ta sanya Zinatu ta yi firgigi, kamar wacce aka tada daga barci da ruwan sanyi.
Ta waigo cikin kad’uwa, idanunta suka yi arba da Tabawa, mahaifiyarta. Nan take ta dawo cikin hayyacinta. Cikin k’ank’anen lokaci ta ankara da cewa, ashe tun d’azu mahaifiyarta ta gargad’e ta da cewa ta wanke kwanonin da sauri, domin ta samu damar gama girkin abincin dare da sauri saboda tana son zuwa barkar haihuwa. Yanzu ne Zinatu ta gane cewa, ashe ta d’auki dogon lokaci, kusan awa biyu tana zaune, ba ta tab’uka komai ba.
“Inna, don Allah ki yi hak’uri, kaina ne ke d’an sarawa, ba na jin dad’i.” Ta yi k’arya da gangan.
“Ai kuwa lokacin da kika nad’e k’afa kina shara loma d’azu, ai kan naki bai sara ba ko, sai yanzu? To, ki shiga taitayinki, kada ki k’ure ni!” Tabawa ke nan cikin fushi, tana rik’e da wata doguwar tsintsiyar kwakwa a hannu; tana daka wa d’iyarta harara. ‘Daure take da wani zane na kamfala, yana d’auke da daud’a, kamar ya shekara bai ga ruwa ba. Sanye a jikinta kuwa, wata riga ce ta gwanjo, mai kalar d’orawa; amma daud’a ta ci k’arfinta, har ta canza kala zuwa ruwan makuba-makuba. Bakinta kuwa ya yi dashasha da goro!
“Sau nawa na gaya maki cewa ki wanke kwanonin nan da wuri? Ina son kafin magariba in gama tuwon nan, domin ina da uzuri, amma ke ga ki ’yar laushi, kin samu wuri, kin rashe, kina sharholiya.” Ta d’an dakata, sannan ta ci gaba.
“Ni, yanzu ma na fara gane gaskiyar Malam, da kullum yake tsegumin kin k’i aure ne saboda d’an Turancin angulun da ke cikin kanki. Shi ke nan ba ku son aiki, don gadarar kun yi karatun zamani?”
Zinatu, babu abin da ke k’ara dugunzuma mata rai kamar irin wannan k’orafi. Yanzu ma ji take kamar an yafa mata wuta. Wani gululun bak’in ciki ya tokare mata mak’ogwaro. Ba ta koma batun Tabawa ba sai ta fizgo kwano d’aya, ta fara wankewa. Mahaifiyarta kuwa ta shuri takalma, ta k’ara gaba, bayan ta doka mata wani uban tsaki.
Tana k’walla ta gama d’inbin wanke-wanken nan, amma yaya za ta yi da ranta? Nan dai gidansu ne kuma iyayenta ne take tare da su, ba wasu bare ba. To, amma saboda me mahaifiyarta ke mata gorin abinci? Wannan abu na d’aure wa Zinatu kai matuk’a.
Duk da cewa ta kammala wanke-wanken kwanonin, sai ta samu kanta zaune a kujera, ta kasa tashi daga wurin. Wannan abin bak’in ciki da ke dabaibaye ta, ya saka ta cikin k’unduttu; dalili ke nan ya sanya ta ci gaba da tunano hirar da suka yi jiya da k’awarta. K’awarta ce Balaraba ta k’ara tabbatar mata da cewa, lallai ita da samun sauk’in irin wad’annan tsegunguma sai ta yi aure ko kuma wani sanadi ya zo, yadda za ta rabu da iyayenta.
(Za a ci gaba ranar Litinin, in sha Allah)
———————————-
© #Bashir_Yahuza_Malumfashi
Laraba 13-06-1442 (Hijriyya)
27-01-2020 (Miladiyya)
———————————-