Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen shekarar 2015 Injiniya Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar PDP inda ya koma sabuwar jam’iyyar NNPP.
Abba Gida-Gida ya sanar da ficewarsa ne daga jami’yyar PDP a wani taro a ofishinsa da ke mazaɓar Diso da ke yankin ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.