Wasu ’yan ta’adda dauke da makamai sun kai mummunan hari a wasu ƙauyuka da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano, inda suka kashe sojoji biyu tare da sace shanu sama da guda 100, abin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da fargaba.
Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa harin ya auku ne da tsakar dare a wasu garuruwa da ke makwabtaka da Jihar Katsina. Maharan sun shigo yankin ne a kan babura sama da 37, lamarin da ke nuna tsari da haɗin kai a harin da suka kai.
Shaidun gani da ido sun ce duk da yawan maharan, ba a samu rahoton sace ko jikkata fararen hula ba. Sai dai sun tabbatar da cewa ’yan ta’addan sun shafe tsawon lokaci a yankin, inda suka tattara shanun kafin su bar wurin da kusan wayewar gari.
Kashe sojojin biyu ya ƙara tayar da hankula, musamman ganin cewa yankin na fama da barazanar hare-haren ’yan bindiga tun a ’yan kwanakin nan. Al’umma sun bayyana damuwa kan yadda tsaron yankin ke kara tabarbarewa duk da kokarin jami’an tsaro.
Bayan harin, mazauna yankin sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da hukumomin tsaro da su gaggauta tura karin jami’an tsaro zuwa yankin, tare da daukar matakan da za su hana maimaituwar irin wannan hari.
Sun kuma bukaci a samar da tsaro na dindindin a yankunan da ke makwabtaka da Jihohin Katsina da Jigawa, domin kare rayuka da dukiyoyin manoma da makiyaya, da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
