Wasu yan bindiga da ake zargin yan daba ne na siyasa sun kai hari kan tawagar jagoran jam’iyyar African Democratic Party (ADC) a yankin Kudu maso Kudu, Chibuike Amaechi, a ranar Juma’a a Jihar Rivers.
Lamarin ya faru ne lokacin da tsohon Ministan Sufuri kuma tsohon gwamnan Jihar Rivers ke kan hanyarsa ta zuwa garuruwansa na Ubima da Omuanwa a karamar hukumar Ikwerre domin yin rajistar e-registration a matsayin mamba na jam’iyyar ADC.
Rahotanni sun nuna cewa tun kafin Amaechi ya isa garin, wasu matasa dauke da makamai da ake zargin mambobin kungiyar tsaro ta sa kai da aka fi sani da OSPAC sun kafa shingen hanya, inda suka rika mayar da motocin bas da ake zargin suna dauke da magoya bayan ADC da suka zo domin halartar ziyarar.
Haka kuma, an ruwaito cewa a daren ranar Alhamis wasu da ba a san ko su waye ba sun kona ofishin mazabar jam’iyyar ADC da ke Ubima, garin da Amaechi ya fito.
Majiyoyi sun kara da cewa maharan sun shigo garin dauke da manyan makamai domin hana zuwan tsohon gwamnan. Sun rika harbe-harbe a cikin al’umma tare da harbin kofar gidan iyalansa da harsasai.
A ranar Juma’a da rana, lokacin da Amaechi ya iso domin shiga garin nasa, yan bindigar sun tare tawagarsa. Sai dai jami’an tsaro da ke cikin tawagar suka yi artabu da su.
Wata majiya daga cikin tawagar ta bayyana cewa bayan jami’an tsaron sun nuna karfin makamai fiye da na maharan, sai yan bindigar suka tsere zuwa cikin daji.
Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyarsa da suka hallara domin shaida rajistar, Amaechi ya bukace su da su kasance masu zaman lafiya.
Ya kuma gode wa Kwamishinan Yan Sanda, Daraktan Hukumar DSS, da kuma Kwamandan NSCDC saboda gaggawar daukar mataki da suka yi, yana mai cewa sun nuna kwarewa wajen shawo kan lamarin.
Amaechi ya bukaci mambobin jam’iyyar da kada su shiga tashin hankali, yana mai cewa aikin bincike, kamawa da gurfanar da wadanda suka aikata harin na hannun jami’an tsaro ne.
Ya kuma yi kira ga gwamnan jihar Rivers da ya kara kokari wajen samar da ingantaccen tsaro a sassa daban-daban na jihar domin hana tabarbarewar doka da oda.
