Wata budurwa yar Kaduna ta damfare saurayin ta N200,000 da suka hadu a Facebook.

Wannan rahoto daga Dandalin HOME OF SOLANCE in da saurayin yace sunyi alakwari da budurwan tashi a zai zo Kaduna domin shi sonta yake kuma aurene a ransa ba wasa ba. Ita kuwa ashe so take ta mai a sha ruwan suntsaye inda.

Acewar sa tabakin shugaban dandalin HOME OF SOLANCE waton Jamila Ibrahim ta rubuta yace a rufe sunan sa kuma a wannan Dandalin suka hadu da budurwar tace masa ita yar kaduna ce, ana sauran kwana daya zai je Kaduna zai ta kirashi tana sheka ubar kuka hankalin sa ya tashi bayan ta sanar dashi cewa masu garkuwa da mutane sunyi garku da mahaifin ta sun bukaci a basu kudin fansa har Naira Miliyon Biyu Da Rabi 2,500,000M kuma a halin da ake ciki suna da Miliyon biyu suna neman cikiton Naira dubu N500,000.

Haka dai saurayin washe gari ya hada Naira Dubu Dari Biyu N200,000 har da sayar da wayarsa domin share hawayen budurwasa ya tura ma ta kudin mahaifiyar ta da yayunta suka masa godiya da abun da ya musu, akan washe gari ranar Lahadi zai je kaduna domin yayi musu jajen abin da ya faru.

Gari na wayewa ya nemeta sama da kasa wayar ta a kashe ya duba manhajar WhatsaApp anan ma ya same kasan ta blocked nashi.

Sai dai mutane da dama sun bashi shawari akan yaje chajin ofis ya shigar da kara hakan kuma ya garzaya zuwa kotu domin a dawo masa da kudin sa.

Ga cikakken bayanin kamar yanda aka wallafa a Dandalin HOME OF SOLANCE.

 

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version