Wani rahoto daga shafin BBC Hausa ya rawaito ta bakin ma’aikacin su mai suna Khalifa Dokaji yana cewa.
Rundunar yan sandan Jihar Kano a Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Auwalu Awaisu mai shekara 19 bayan mahaifinsa ya lakaɗa masa duka a daren ranar Juma’a da ta gabata.
‘Yan sandan sun ce matashin ya mutu ne a ranar Litinin a Asibitin Murtala sakamakon dukan da mahaifin nasa ya yi masa a ka da kuma cikinsa.
A cewar ‘yan sandan, mahaifin Auwalu mai suna Awaisu Auwalu na zargin dan nasa Auwalu Awaisu wato Abba da batan wasu kudadensa a shagonsa.