Wani matashi dan jihar Delta zai aure mata biyu a lokaci daya

Matashin dai mai suna Samson Uthuko Uloho dan jihar Delta a kudan cin Nigeria ya shirya tsaf dan auran yan mata 2 a lokaci daya.

Wanda a halin yanzun har an sa ranar auren ranar a sabar 11 ga watan April 2021 a karamar hukumar Isoko ta kudu.

Katin Gayyatar Aure



Sunayen yan matan kuwa sune Evelyn da Faith, tuni katin gayyatar daurin auren ya bazu a shafukan sada zumunta inda kowa yana tofa albarkacin bakin sa. Ga muharar shafin twitter akan wannan katin gayyatar wanda shafin wani mai suna @wakajugde ya wallafa.



Wannan batu a arewancin Nigeria abune wanda matasan arewa sun jima da yin hakan kuma ya fara zama ruwan dare sai dai kudan cin Nigeria abune bako wanda baโ€™a saba yin sa ba.

Haka zalika a addinin kirista wannan batun babban lamarine dan kuwa auren mata biyu kamar haramun ne a garesu saidai gashi shi wannan matashi zai aure mata biyu a lokaci guda.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
โ†‘
Exit mobile version