Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kafa wata sabuwar cibiyar dakarun tsaro a yankin Tidibale, wani babban mataki na gaggawa da nufin dakile barazanar ’yan bindiga da suka addabi al’ummar yankin.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar kalubalen tsaro inda mahauta ke kokarin tursasa wa mazauna kauyuka barin muhallansu ta hanyar amfani da makamai da barazana.
A cikin wata sanarwa da Abubakar Bawa, shugaban sashen yada labaru na ofishin gwamnan jihar ya sanya wa hannu, gwamnatin ta bayyana cewa wannan sabuwar cibiya za ta tallafa wa ayyukan jami’an tsaro da ke Karamar Hukumar Isa. Manufar ita ce samar da dakarun da za su kasance a shirye a kowane lokaci don fatattakar masu tada kayar baya.
Gwamnatin jihar ta yi amfani da wannan dama don karyata wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta (Social Media), wanda ake ikirarin cewa mutanen Tidibale ne ’yan bindiga suka kora daga gidajensu.
Gwamnati ta fayyace cewa abin da aka gani a bidiyon ba guduwa ba ne; kwashe mutanen aka yi domin kare rayukansu.
“Tabbas mutanen Tidibale ne, amma ba ’yan bindiga ne suka koro su ba,” in ji sanarwar.
“Gwamnati ce ta kwashe su na wucin-gadi zuwa babban birnin karamar hukuma bayan an sami bayanan sirri (Intelligence reports) kan yiwuwar fuskantar harin ’yan bindiga a yankin.”
Bayan tabbatar da cewa an shawo kan matsalar, sanarwar ta bayyana cewa tuni an mayar da mutanen zuwa kauyensu na Tidibale. A halin yanzu, jami’an tsaro na nan daram a yankin suna gudanar da sintiri domin tabbatar da doka da oda tare da hana sake afkuwar duk wata barazana.
Jihar Sokoto na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamman Najeriya da suka dade suna fama da matsalar ’yan bindiga masu kisa da garkuwa da mutane. Wannan sabon mataki na kafa cibiyar tsaro a Tidibale na daya daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na sauya salon yaki da ta’addanci zuwa amfani da bayanan sirri da kuma samar da dakarun gaggawa.
