Trump Ya Bai Wa Iran Wa’adin Kwana Biyu Ta Amince da Yarjejeniya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bai wa Iran wa’adin kwanaki biyu ta amince da wata yarjejeniya tare da buɗe mashigar Strait of Hormuz, ko kuma ta fuskanci hare-haren soji.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya tunatar da cewa tun farko ya bai wa Iran wa’adin kwanaki 10 domin ta amince da yarjejeniyar ko ta buɗe mashigar Hormuz, yana mai cewa yanzu lokacin ya kusa ƙarewa.

“Ku tuna lokacin da na bai wa Iran kwanaki 10 ta amince da yarjejeniya ko ta buɗe mashigar Hormuz. Yanzu lokaci na ƙarewa,” in ji Trump.

Ya ƙara da cewa, “Yanzu saura sa’o’i 48 kafin su fuskanci mummunan martani.”

A ranar 27 ga watan Maris ne Trump ya sanar da dakatar da kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Iran na tsawon kwanaki 10, domin ba da damar cimma wata yarjejeniya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version