Tinubu Ya Nada Amb. Ismail Abba Yusuf a Matsayin Shugaban NAHCON

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaba/Kwamishinan Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON).

Nadin nasa na jiran amincewar Majalisar Dattawa kamar yadda sashe na 3(2) na Dokar NAHCON ta shekarar 2006 ya tanada.

Shugaba Tinubu ya aike da wasika ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, inda ya bukaci a gaggauta tabbatar da nadin Ambasada Yusuf domin maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a wannan mako bayan shafe kimanin watanni 14 a kan mukamin.

Ambasada Ismail Abba Yusuf gogaggen jami’in diflomasiyyar Nijeriya ne, wanda ya taba zama Jakadan Nijeriya na musamman kuma cikakken wakili a Jamhuriyar Turkiya daga shekarar 2021 zuwa 2024.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version