Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci sabbin jami’an da za a zaba cikin Kwamitin Gudanarwa na kasa (NWC) na All Progressives Congress (APC) da su gudanar da aikinsu cikin tawali’u, adalci da cikakken biyayya ga manufofin jam’iyyar.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a birnin Abuja yayin babban taron ƙasa na jam’iyyar da aka shirya domin zaɓen sabbin shugabanni na kasa. Taron na wannan shekarar ya gudana ne karkashin taken “Unity in Progress: Consolidating the Renewed Hope Agenda.”
Tinubu ya ce taken taron yana tunatar da ‘ya’yan jam’iyyar cewa babu wani ci gaba mai ɗorewa sai da haɗin kai. Ya jaddada cewa waɗanda za su jagoranci jam’iyyar dole su kasance masu gaskiya, jarumtaka da hangen nesa domin ci gaban jam’iyyar da demokuraɗiyyar Najeriya.
“Ga duk waɗanda za a zaba yau, ku rike wannan amanar da tawali’u da adalci tare da cikakken biyayya ga manufofin jam’iyyar. Makomar APC da kuma demokuraɗiyyar Najeriya na hannunku,” in ji shugaban ƙasar.
Tinubu ya kuma bayyana cewa jam’iyyar ta samu karbuwa sosai a cikin shekaru biyu da suka gabata, inda gwamnoni, sanatoci da ‘yan majalisa da dama daga wasu jam’iyyu suka koma APC. A cewarsa, hakan na nuna irin amincewar da jama’a ke da ita ga jam’iyyar.
Har ila yau, ya buƙaci sabbin shugabannin jam’iyyar su tabbatar da gudanar da tsarin jam’iyya cikin gaskiya da tsari, musamman ta hanyar gina sahihin kundin bayanan membobin jam’iyyar a faɗin ƙasa.
Shugaban ƙasar ya yaba wa kwamitin shirya taron na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari da Anyim Pius Anyim bisa kokarin da suka yi wajen shirya taron cikin nasara.
Tinubu ya kuma yabawa mata musamman na jam’iyyar APC, yana mai cewa rawar da suke takawa na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa jam’iyyar da demokuraɗiyyar kasa.
Karanta: APC Ta Fitar da Farashin Fom din Takarar Zaben 2027
“A jam’iyyar APC dole ne mu kara bude kofofi ga mata domin su jagoranci, su yi tasiri a manufofi, kuma su taimaka wajen gina demokuraɗiyyar Najeriya,” in ji shi.
