Tinubu Ya Gana da Shugabannin Tsaro Bayan Sabbin Hare-Haren Yan Ta’adda a Najeriya

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Ministan Tsaro da kuma manyan shugabannin rundunonin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa da ke fadar shugaban kasa a habuuja ranar Alhamis, biyo bayan sabbin hare-haren yan ta’adda da suka kara tayar da hankalin jama’a.

A taron wanda ya ɗauki kusan sa’o’i biyu, an samu halartar Ministan Tsaro, Christopher Musa, da shugabannin rundunonin tsaro da kuma Sufeto Janar na Yan Sanda, Olatunji Bello.

Wannan shi ne karon farko da aka gudanar da irin wannan taro tun bayan nadin sabon Sufeto Janar na Yan Sanda.

Taron ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsalolin tsaro a sassa daban-daban na kasar, musamman bayan rahotannin kashe wasu manyan kwamandojin sojoji a wuraren da ake gudanar da ayyukan yaki da ta’addanci.

Daga cikin hare-haren da suka faru kwanan nan akwai farmakin da yan ta’adda suka kai a kauyen Ngoshe da ke Borno State, wanda ya yi sanadin sace mutane da dama, da kuma wasu hare-hare daban a yankin Konduga.

A makon da ya gabata yayin bude baki da shugabannin tsaro, Shugaba Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen ta’addanci a kasar.

“Najeriya za ta yi nasara a yakin da take yi da yan ta’adda duk da wadannan hare-hare. Ba za mu mika wuya ga masu tada kayar baya ba,” in ji shugaban.

Ganawar ta Tinubu da shugabannin tsaro ta zo ne kwana guda bayan Ministan Tsaro ya gana da su a hedikwatar Ma’aikatar Tsaro domin tattauna sabbin hanyoyin da za a bi wajen karfafa yaki da yan ta’adda.

A yayin taron, Ministan Tsaro ya bayyana cewa sun amince da sake nazarin dabarun yaki domin kara inganta nasarar rundunar sojojin Najeriya duk da asarar da aka samu a wasu lokuta.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version