Aisha da Ahmad, masoya da suka fara soyayya ta hanyar fitowa a fim a masana’antar Kannywood, sun kulla tarihi mai kyau wanda ya kai su ga zama miji da mata. Masoyan sun fara shahara ne a shafukan sada zumunta musamman ta hanyar fina-finan soyayya da kuma TikTok da suke yi tare. Wannan soyayya ta zama abin alfahari ga masoyansu da dama.
Ranar Juma’a, 18 ga watan Janairu 2025, za a ɗaura auren Ahmad (wanda ake yi wa laƙabi da Malam Onshaz) da Aisha (Aysha Lily). Wannan bikin aure na musamman yana dauke da shiryawa ta fannoni daban-daban, daga ranar kauyawa zuwa ranar ball, har da daren Arabian night da kuma kammalawa da dinner a ranar ƙarshe.
Masoyansu suna fatan Allah Ya sa auren ya kasance cike da albarka da kwanciyar hankali. A lokaci guda, ana kira ga ƴan fim su yi koyi da su, su ma su kawo ƙarshen soyayyar fim da aure don inganta al’adun aure da zamantakewa a tsakanin masu sha’awar fina-finai.
Allah Ya albarkaci wannan masoya. Amin.