Sojojin Najeriya Sun Tarwatsa Harin ISWAP a Yobe, sun kashe  yan ta’adda 20

Sojojin Rundunar Hadin Kai ta Arewa Maso Gabas (Operation HADIN KAI) sun tarwatsa wani hari da yyan ta’adda suka kai a Goniri, Jihar Yobe, inda suka kashe fiye da yan ta’adda 20 a wani fafatawa mai tsanani da aka yi

Rahotanni daga rundunar soji sun bayyana cewa yan ta’addan da ake zargin suna daga kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun kai farmaki ne akan sojoji da ke yankin karkashin sashe na 2 na aikin.

An fara lura da yan ta’addan yayin da suke matsowa daga kauyen Goniri da kuma Ngamdu junction don ganin sun kewaye rundunar sojin. Sai dai sojojin sun yi amfani da karfin wuta da dabarun yaki na musamman wajen tarwatsa hare-haren.

Sannan an tura karin sojoji yayin da Rundunar Sama ta Operation HADIN KAI ta bada goyon baya daga sama, wanda ya rage karfin yan ta’addan.

A yayin musayar wuta, yan ta’addan sun yi rauni matuka kuma aka tilasta su tserewa, inda suka bar gawawwakin su da makamai a filin. An gano babban kwamandan ISWAP mai suna Abu Yusu, Munzir na Dursula, a cikin wadanda aka kashe.

Sojojin sun kwato makamai da kayan yaki da dama kamar AK 47, bindigogi, bam-bam, da sauran kayan yaki daban-daban.

Bayan harin, sojojin sun ci gaba da gudanar da ayyukan tsabtace wurare da sintiri a yankin Gwaigomari da ke cikin Timbuktu Triangle, inda aka samu wasu gawawwakin yan ta’addan.

An kai wasu sojoji da suka ji rauni asibiti inda suke samun kulawar lafiya, kuma an tabbatar suna cikin yanayi mai kyau. Hukumar soji ta tabbatar wurin yana karkashin cikakken ikon rundunar Operation HADIN KAI, yayin da suke kara inganta sintiri da bincike a unguwanni da ke kewaye.

Babban kwamandan rundunar ya yabawa jarumtakar sojojin, yana mai karfafa su da su ci gaba da yakin neman tabbatar da zaman lafiya da kawar da ta’addanci a arewa maso gabas.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version