Sojoji Sun Gargadi Jama’a Kan Karin Yan Kunar bakin wake Bayan Harin Bam a Maiduguri

Sojojin Najeriya karkashin Operation Hadin Kai sun gargadi al’ummar Maiduguri, a jihar Borno State, kan yiwuwar sake samun hare-haren yan kunar bakin wake bayan mummunar fashewar bam da ta faru a daren Litinin.

A cewar rundunar sojin, hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 23 tare da jikkata sama da 100, yayin da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai harin ta hanyar amfani da na’urorin fashewa (IEDs).

Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sun faru ne da misalin karfe 7 na yamma, jim kadan bayan bude baki, inda aka kai hari wurare masu cunkoso ciki har da kofar jami,ar Maiduguri Teaching Hospital, kasuwar Monday da kuma yankin Post Office.

Sojoji tare da jami’an Nigeria Police Force da sashen kwantar da bama-bamai sun gaggauta isa wuraren da abin ya faru, inda suka killace wuraren domin hana karin hatsari.

Hakazalika, jami’an agajin gaggawa na National Emergency Management Agency sun kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibitoci ciki har da General Hospital, Specialist Hospital da UMTH domin samun kulawa.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Naziru Abdulmajid, ya kai ziyara wuraren domin duba yadda ake tafiyar da aikin ceto da tsaro.

Rundunar sojin ta bukaci jama’a su kasance cikin shiri, su guji wuraren cunkoso, tare da kai rahoton duk wani motsi ko abu da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro.

Ta kuma jaddada kudirinta na ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version