Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana matukar alhini da damuwa kan rahotannin da ke cewa an kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei. A cikin sakon ta’aziyya da ya fitar, Putin ya bayyana lamarin a matsayin wani babban al’amari da zai iya tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya.
Kamfanin dillancin labaran Rasha, TASS, ya rawaito shugaban na Rasha yana cewa kisan jagoran addinin na Iran “kisan gilla ne da ya saɓa wa dokokin duniya da kuma ka’idojin mutunta rayuwar dan’adam.” Ya kara da cewa irin wannan mataki na iya jawo tashin hankali a tsakanin kasashe tare da barazana ga zaman lafiyar duniya.
Putin ya kuma jaddada cewa kasarsa ta Russia tana goyon bayan mutunta dokokin kasa da kasa, musamman dokokin da ke kare rayuwar shugabanni da kuma jagororin addini. Ya ce kashe shugabanni ta hanyar tashin hankali ba zai taimaka wajen warware rikice-rikice ba, sai dai ya kara tsananta matsalolin siyasa da tsaro.
A cewarsa, ya kamata al’ummar duniya su mayar da hankali wajen karfafa tattaunawa da diflomasiyya domin rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya. Putin ya yi kira ga kasashen duniya da su guji daukar matakan da za su iya haddasa rikici ko yaki.
Kasar Iran dai na daga cikin manyan kawayen Rasha a fagen siyasa da tattalin arziki. A cikin ‘yan shekarun nan, kasashen biyu sun kara karfafa alakarsu ta fuskar tsaro, tattalin arziki da makamashi. Haka kuma a shekarar da ta gabata, Moscow da Tehran sun rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya ta haɗin gwiwar soja da nufin karfafa tsaron yankin da kuma bunkasa huldar su ta diflomasiyya.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa dangantakar Rasha da Iran ta kara karfi musamman bayan takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa kasashen biyu.
Wannan hadin gwiwa ya hada da cinikayya, makamashi, fasahar soja da kuma hadin kai a wasu batutuwan siyasar duniya.
Putin ya kammala da cewa mutuwar Khamenei babban rashi ne ga al’ummar Iran, tare da kira ga dukkan bangarori da su yi kokarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
