Shirin Gidan Badamasi ko Asibitin Magance Hawan Jini


Sharhi Daga: Bashir Yahuza Malumfashi
Sunan Fim: Gidan Badamasi
Labari: Falalu A. Dorayi
Tsara Labari: Nazir Adam Salih
Shiryawa: Falalu A. Dorayi da Nazir Adam Salih
Daukar Nauyi: Nazir Adam Salih
Shekarar Shiryawa: 2018


Mai Sharhi: Bashir Yahuza Malumfashi
Masu hikimar magana suna cewa, ana bikin duniya kuma ake na kiyama, idan an taba kida, sai kuma a taba karatu. Wadannan azancin magana ne suka zo a tunanina a lokacin da na kuduri aniyar rubuta sharhi kan fim din Gidan Badamasi – fim din barkwanci, mai dogon zango da ake nunawa duk daren Alhamis a tashar talabijin ta Arewa24.


Kamar yadda bincikena ya nuna, Gidan Badamasi shi ne fim din Hausa mai dogon zango na farko da aka fara shiryawa a duk duniya. An fara daukar Zango na Farko na fim din Gidan Badamasi a ranar 5 ga watan Maris, 2018 kuma yana dauke da sassa 14 da aka fara nunawa a shekarar 2019. Haka kuma an fara daukar Zango na Biyu a ranar 12 ga watan Maris na 2020, kuma yana dauke da sassa 13, wanda kuma ake kan nunawa a tashar talabijin ta Arewa24.


Fim ne da ke ba da labarin rayuwar attajirin Bahaushe a zamanance, inda a tare da haka aka hasko rayuwar Alhaji Badamasi da ta iyalinsa, musamman abin da ya shafi zamantakewa da rayuwar yau da kullum. Labarin ya yi naso, inda ya bayyana halayen mutane mabambanta da suka danganci shashanci, ashararanci, ballagazanci, karuwanci, hadama, kwadayi, gaskiya da rashin gaskiya, amana da cin amana, zamba, rowa, sata, bokanci da sauransu.


An warware jigon fim din ne kacokan da salon barkwanci, ta yadda a kowane kalami ko aiki ko motsi da dan wasa ko ’yar wasa za su yi, suna tattare da ban dariya. Wanda ta haka ne mai kallo zai kasance cikin tsintar mabambantan darussa – ya nishadantu a bangare guda, sannan kuma ya karu da wani ilimi na rayuwar ’yan zamani a daya bangaren.


Kamar yadda labarin yake, Alhaji Badamasi (Magaji Mijinyawa) wani matsolon attajiri ne, wanda ya yi gwagwarmayar rayuwa ya tara abin duniya. Daga bisani laulayin jiki ya sa yake rayuwa a keken guragu. Ya tara ’ya’ya maza da mata, a sakamakon auri-saki da ya sha yi a rayuwarsa.

Kamar yadda ya fada da bakinsa, ya auri mata 12 a rayuwarsa. Ta fannin aiki ko sana’a kuwa, ya ce ya yi dakon giya, ya yi leburanci da sauransu.
Fim din Gidan Badamasi ya ta’allaka ne kacokan kan rayuwar shi Alhaji Badamasi da ta iyalinsa da barorinsa a gida da waje. Duk wani abu da ya wakana a fim din, yana da dangantaka da Badamasi kai tsaye ko a kaikaice.


Jerin ’yan wasan da ke fim din sun dace da guraben da aka zaba masu. Irin yadda Hajiya Zulai (Hajiya Jummai), a matsayinta na uwargidan Alhaji Badasi ta rika tafiyar da al’amuran gidan, ya nuna kwarewarta a wasan barkwanci, duk kuwa da cewa a can baya ba a fina-finan barkwanci take fitowa ba.


Babban yaron gidan Alhaji Badamasi, Taska (Falalu Dorayi), ya taka rawa sosai wajen bayyana halayen yaran gida a gidan attajirai. Ya san yadda ake kulla munafunci, alaye, kamar kuma yadda ya iya mu’amala da maigida da ’ya’yansa masu mabambantan halaye.


A halayen Bazuka (Mustafa Nabaraska), an bayyana wani tantirin dan bariki, wanda ya kware wajen sana’ar holewa. Ita kuwa Sabira (Hauwa ’Yar Auta) ta wakilci irin gaulaye kuma kauyawan matan nan da ke zuwa birni barance. Dankwambo (Nura Dandolo), a matsayinsa na babban dan Alhaji Badamasi da ya shiga duniya, ya wakilci irin tantiran nan da suka buga bariki kuma suka kasa tsinana wa kansu komai. Rayuwarsa na nuna cewa babu nasara ga matashin da ya zabi rayuwar holewa da rakashewa.


A rayuwa da halayen Zaidu (Aminu Mirror), an bayyana mana irin halayen masu fakewa da guzuma suna harbin karsana, masu halayen Annabi Musa a fuska, Fir’auna a zuci. Shi kuwa Adhama (Tijjani Asase), a fim din yana wakiltar irin shashashan mutanen nan da ba su da wani burin ci gaba a rayuwarsu. Ga kato har kato amma bai amfana wa kansa komai, matarsa ke yi masa linzami. Ga Zuly (Umma Shehu), wacce ta kasance “Babbar Yarinya.” Rayuwarta na wakiltar irin sangartattun ’ya’yan attajirai da ke sarrafa rayuwarsu yadda suka ga dama a bariki, ba tare da kwabar iyaye ba.


Ga Indiye (Sani Dangwari), wanda ya haska rayuwar kananan kabilu a dangantakarsu da Hausawa. Azima (Hauwa Ayawa) ta kasance ’yar lele, wadda ke wakiltar rayuwar dalibai a gidan attajirai. Gimba (Nasiru Muhammad Horror) na nuna yadda agola ke samun gata da walawa a gidan auren mahaifiyarsa. Hauwa (Hadiza Kabara), kamar yadda ta fito, tana nuna yadda soyayya ke taka rawa a zukatan wasu mata. Dubi dai yadda ta kasance diyar attajiri amma ta kare da auren mummunan kato, barawo, wanda bai tsinana mata komai.
Shi kuwa Sha’arani (Ibrahim Yala Hayin Banki) yana wakiltar irin alarammomin nan da ke mayar da karatunsu ga tsibbu. A yayin da Sulaiman Bosho ke wakiltar rayuwar bokaye – karya da karairaye da barazana da ban tsoro yayin gudanar da sana’arsu.


A rayuwar Tani (Hadiza Gabon) an nuna ma’anar karin maganar nan ta Hausa da ke cewa da haihuwar yuyuyu, gara da daya kwakkwara; domin kuwa duk tarin ’ya’yan Alhaji Badamasi, ita kadai ta fita zakka, ta yi karatu kuma har ta zama kwararriyar likita. Ta kasance abin alfahari da kwatance ga mahaifinta da ma ’yan uwan nata. Hakan kuma ke kara nuna cewa ba lallai sai da namiji ne zai iya amfanar al’umma ba, tun da ga su Dankwambo yayyenta maza sun zama shashashai, ita kuwa ta zama ta kirki.
Abin mamaki, ga gajere ba yaro ba, nakasa ba kasawa ba – ina maganar Dokta Kumo, wanda duk da yanayin halittar jikinsa amma ya yi karatu ya zama cikakken kuka kwararren likita, alhali ga katti masu lafiyayyen jiki irin su Bazuka sun zama ballagazazzu. Wannan ke nuna cewa himma ba ta ga raggo. Duk abin da mutum ke son ya zama a rayuwa, idan ya maida hankali zai zama.


Sauran ’yan wasa da suka yi kokari kuma suka sanya armashi ga fim din sun hada da Ali Boy (Nasiru Aliku Koki) da Na’Allah (Ado Gwanja) da Magaji Dauri (Usaini Sule Koki) da Adnani Sumail (Rabi’u Daushe) da sauransu.
Abin tambaya kuma shi ne, shin wadanne fa’idoji za a iya samu daga fim din Gidan Badamasi? Babu shakka akwai fa’idoji da suka hada da: Fim din na sanya nishadi da farin ciki ga duk mai kallonsa, musamman saboda yadda yake cunkushe da barkwanci. Likitocio ma sun bayyana cewa ga duk mai yawan samun farin ciki ko annashuwa, ba zai rika samun damuwa ko ciwon hawan jini ba. Dalili ke nan ma wasu ke ganin cewa Gidan Badamasi tamkar asibiti ne da ke maganin hawan jini.


Fim din Gidan Badamasi, a matsayinsa na Hausa mai dogon zango kuma na farko a irinsa na barkwanci, ya kawo kalubale da sauyi a duniyar shirya fina-finan Hausa. Hakan ya sanya harshen Hausa ya kara samun bunkasa da tagomashi a duniyar adabi. Wannan dalili ne kuma ya sanya ya samu amsuwa a duk duniya, musamman duk inda al’ummar Hausawa ko masu fahimtar Hausa suke zaune.


Gidan Badamasi ya kasance sha-kundum, ma’ana bai da gefe ga masu kallonsa, domin kuwa yara da manya, maza da mata za su iya kallonsa hankali kwance ba tare da tsoron wani abu ba. Ba kamar wasu fina-finai ba da ake yi wa wasu rukunan mutane iyaka, a ce sai dan shekara kaza zuwa kaza za su kalla.


Gidan Badamasi ya haifar da wata sara, inda duk wani magidanci marar adalci ko attajirin marowaci ake kiransa da Gidan Badamasi. Hakan ke nuna mana cewa lallai halayyar rowa da rashin adalci ba dabi’un kwarai ba ne.


A duk lokacin da za a gabatar da wani al’amari, musamman ma bako a cikin al’umma ba za a rasa fuskantar kalubale ba. Fim din Gidan Badamasi ma bai tsira daga haka ba, musamman wasu na yi masa wani gani-gani, cewa ya zo da wani salo daban da zai iya sauya akalar nishadin Hausawa. Wasu ma na ganin cewa ana so ne a nuna Bahaushe da wata mummunar fuska ta auri-saki. Masu irin wannan fahimta sun alakanta rayuwar Alhaji Badamasi, inda ya haifi ’ya’ya da yawa kuma suka kasance karkatattu, marasa amfani.
Da na tambayi furodusan fim din Gidan Badamasi irin kalubalen da suka fuskanta game da shirin, sai ya amsa da cewa:
“Kalubale na farko shi ne lokacin da Zango na Farko ya fita mun sanya dariya a bayan fage, kamar yadda yake bisa al’ada idan ana fim din barkwanci. To, sai dai nan da nan ’yan kallonmu suka ki karbar wannan dariya da ke bayan fage; suka yi ta korafi sai da muka cire ta sannan aka samu lafiya.


“Kalubale na biyu kuma shi ne, takun-saka da muka samu da Hukumar Tace Fina-Finai, wacce ta yi kokarin dakatar da fim din bisa cewa dole sai an yi masa rijista, duk kuwa da cewa ba ta da hurumi a kan fina-finai masu dogon zango da aka yi su don nunawa a gidajen talabijin na satalayit.”
Ya ci gaba da cewa “sai kuma kaulubale na uku, wanda muna cikin fim din aka shiga kullen zama gida saboda annobar Kurona, inda da kyar muka samu damar gama daulkar Zango na Biyu saboda ka’idojin haka da Gwamnatin Jihar Jigawa ta matsa mana lallai sai mun fita daga jihar, domin bin doka da oda. Wannan ya sa mun gama aikin a gaggauce, haka nan ya kawo mana jinkiri wajen tace hotunan zangon na biyu, domin lokacin da muka dawo gida ko’ina ba a fita aiki.”


Koma dai yaya ake ciki, fim din Gidan Badamasi ya ciri tutu kuma ya zama mai amfani da amfanarwa ga al’umma, musamman ma wajen samar da kafar nishadi, bunkasa adabin Hausa, samar wa wasu hanyar sana’a da sauransu.

© Bashir Yahuza Malumfashi (+234 8065576011)
Talata, 21-12-1441 (Hijriyya)

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version