Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Usman Kusfa Rigi-Rigi, ya rasu bayan ya sha fama da gajeriyar jinya a Asibitin Sojoji na 44 da ke Jihar Kaduna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Sheikh Usman Kusfa Rigi-Rigi ya rasu ne bayan kwana da dama yana karɓar kulawar likitoci sakamakon rashin lafiyar da ta addabe shi.
Rasuwarsa ta jefa al’ummar Musulmi da mabiyansa cikin alhini, musamman ganin irin gudummawar da ya bayar wajen wa’azi da koyar da addini tsawon rayuwarsa.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 57 a duniya, inda ya bar mata huɗu da ‘ya’ya 37. An bayyana Sheikh Usman Kusfa Rigi-Rigi a matsayin malami mai jajircewa, wanda ya shahara da tsayawa kan gaskiya da kuma faɗakar da al’umma kan harkokin addini da tarbiyya.
Mutuwarsa ta haifar da jimami a tsakanin malamai, almajirai da jama’a, inda da dama suka rika bayyana ta’aziyya da addu’o’i, suna roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, Ya kuma ba iyalansa da dukkan masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Ana sa ran za a gudanar da jana’izarsa bisa koyarwar addinin Musulunci, yayin da ake ci gaba da addu’a domin Allah Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya kuma saka masa da alheri a lahira.
