Sheikh Dahiru Usman yace bana za’a gudanar da Tafsiri ne a Bauchi ba tareda Anje Kaduna

Tafsirin wata Ramadana da babban Malamin addini Sheikh Dahiru Usman Bauchi R.T.A yake yi a Kaduna wannan shekarar a garin Bauchi zai yi.

Wannan sanarwan mun samu daga wurin mai daukan tafsirin a kowane shekara Usman Shuaibu Kunsal (Mai Kasuwa) wanda ya shaida mana cewa Sheikh Dahiru ya sanar da manema labarai cewa

” Ansamu matsaya gameda Tafsirin bana wanda aka sabayi a Kaduna duk Shekara cikin zantawa da maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi R.T.A yayi da maneman labarai a yau Laraba “

” Shehu ya bayyana cewa Insha Allahu a bana za’a gudanar da Tafsiri ne a Bauchi ba tareda Anje Kaduna ba Shehu ya kara da yace za’a turo masu daukan tafsirin daga Kaduna da Sauran wurare daban daban Inda zasu dauki Tafsirin a watsa a duniya”

Sannan Shehu yaja hankalin cewa kar’a daina Sallar Juma’a Akalla mutum goma Sha biyu, shima Sallan tahajudi da Asham A samu koda mutum bakwai zuwa sama a dunga gudanarda Sallah

Shehu yace Ayi hakurida yanda Allah ya kaddara lamarin Allah yabamu lafiya da zaman lafiya albarkan Manzon Allah S.A.W

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version