Ƙasar Saudiyya ta bayyana shirin fara bai wa miliyoyin raƙuman da ke cikinta fasfo, a wani yunkuri na inganta kulawa da kuma daidaita harkokin kiwon raƙuma a ƙasar.
A cewar jami’an gwamnati, wannan mataki zai taimaka wajen bunƙasa fannin kiwon raƙuma, inganta inganci da kuma samar da sahihin kundin bayanai da za a rika amfani da shi wajen tantance shaida da mallakar raƙuma.
Wata sanarwa da ma’aikatar muhalli, ruwa da noma ta fitar ta nuna fasfon raƙuma, wanda ke da launin kore tare da ɗauke da tambarin ƙasar Saudiyya da kuma hoton raƙumi mai launin zinariya.
A shekarar 2024, gwamnati ta ƙiyasta cewa akwai raƙuma kusan miliyan biyu da dubu dari biyu a faɗin ƙasar.
Raƙuma na da muhimmiyar rawa a al’adu da tattalin arziƙin Saudiyya, inda ake shirya gasar kyau ta raƙuma a yayin bukukuwan shekara-shekara, lamarin da ke ƙara nuna darajar dabbar a rayuwar al’ummar ƙasar.
