Ofishin (NSA) ya musanta zargin sayen sinadarin guba

Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA) ya musanta zargin cewa ya sayo ko ya shigo da sinadarin thallium sulphate, wani sinadari mai tsananin guba wanda ba shi da launi ko wari kuma zai iya kashe mutum cikin dan kankanin lokaci.

Musanta lamarin ya biyo bayan wata wasika da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya aike wa Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, mai kwanan wata 30 ga Janairu, 2026.

A cikin wasikar, El-Rufai ya ce wasu bayanai da suka samu daga shugabannin adawa na nuna cewa ofishin NSA ya sayo kusan kilogram 10 na thallium sulphate daga wani mai sayarwa a Poland.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an mika batun ga Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Kasa (DSS) domin gudanar da cikakken bincike. Haka kuma za a gayyaci El-Rufai da duk masu bayanai masu alaka da zargin domin su gabatar da hujjoji.

Abubuwan da ke cikin wasikar El-Rufai

A wasikarsa, El-Rufai ya bayyana zargin a matsayin abin damuwa ga jama’a, yana mai cewa sinadaran thallium na daga cikin abubuwan da ake takaita su sosai saboda tsananin gubarsu.

Ya nemi a fayyace muhimman bayanai kamar:

Ya ce ya yi tambayoyin ne domin tabbatar da bin ƙa’idoji, tsaro da gaskiya, yana mai cewa amincewar jama’a ga hukumomi na ƙaruwa ne idan ana bayyana gaskiya kan irin waɗannan batutuwa.

Rikicin Ribadu da El-Rufai

Musayar kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Ribadu da El-Rufai ke ƙara dagulewa, duk da cewa a baya sun kasance abokai na kud-da-kud.

Dukansu sun yi fice a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo. A wancan lokaci, Ribadu shi ne shugaban farko na Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), yayin da El-Rufai ya rike mukamin Darakta Janar na Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati kafin daga bisani ya zama minista.

Dangantakarsu ta fara tsami ne a 2011 lokacin da jam’iyyar ACN ta tsayar da Ribadu takarar shugaban kasa matakin da El-Rufai bai goyi baya ba, inda ya marawa tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya a wancan zaben.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version