Reshen Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) a Jami’ar Legas (UNILAG) ya sanar da dakatar da yajin aikin da ba a kayyade lokacin karewarsa ba da ya fara a ranar Talata.
Kungiyar ta bayyana cewa an dakatar da yajin aikin ne bayan shiga tsakani da shugabancin kungiyar na kasa.
A cikin wata sanarwa da shugabar reshen kungiyar, Farfesa Idou Keinde, ta fitar, ta ce an bukaci mambobin kungiyar su bi umarnin shugabannin ASUU na kasa tare da komawa bakin aiki yayin da ake kokarin warware matsalar.
Mahukuntan jami’ar sun kuma bayyana cewa sun bude tattaunawa da kungiyar domin magance matsalolin da suka janyo yajin aikin.
Tun da farko, ASUU-UNILAG ta shiga yajin aiki ne saboda zargin rage albashin malamai na watannin Janairu da Fabrairu, da kuma rashin biyan wasu kudaden alawus-alawus da suka hada da Earned Academic Allowance da kuma Consolidated Academic Tools Allowance (CATA).
Gwamnatin tarayya ta kara wadannan alawus-alawus ne bayan wata yarjejeniya da ta cimma da kungiyar a watan Disamba, wadda ta fara aiki daga watan Janairu.
Kungiyar ta tabbatar cewa ana ci gaba da tattaunawa da mahukuntan jami’ar domin samun mafita mai dorewa ga matsalolin.
