NDLEA Ta Kama Tabar Wiwi Ta Naira Biliyan 10.4 a Lagos

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, ta kama wata babbar tabar wiwi nau’in “Canadian Loud” da aka kiyasta kuɗinta ya kai naira biliyan 10.4 a jihar Lagos bayan an shigo da ita daga ƙasar Canada.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar sun gano tabar wiwin mai nauyin kilo 4,173.5 a tashar jiragen ruwa ta Tin Can Island da ke Lagos yayin gudanar da bincike kan kayayyakin da aka shigo da su cikin ƙasar.

NDLEA ta ce an ɓoye miyagun ƙwayoyin ne a cikin wasu kaya domin kauce wa binciken jami’an tsaro, amma bincike mai zurfi da aka gudanar ya kai ga gano su tare da ƙwace su.

Hukumar ta bayyana cewa kama wannan tabar wiwi wani ɓangare ne na ƙoƙarin da take yi na dakile safarar miyagun ƙwayoyi da kuma kare matasa da al’umma daga illolinsu.

Shugaban NDLEA, Brigadier Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yaba wa jami’an hukumar bisa nasarar aikin tare da jaddada cewa za su ci gaba da yaƙi da masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar.

Hukumar ta kuma tabbatar da cewa bincike na ci gaba domin gano mutanen da ke da hannu wajen shigo da tabar wiwin domin gurfanar da su a gaban kotu.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version