Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya wakilci fitaccen attajirin nan Theophilus Yakubu Danjuma, a bikin kamun kifi na Nwonyo na shekarar 2026 da aka gudanar a garin Ibi, Jihar Taraba.
A yayin bikin, Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa taron al’adun yana wakiltar hadin kai da zaman lafiya, tare da janyo hankalin masu yawon bude ido daga gida da waje, wanda ke kara darajar Taraba a fiskar duniya.
Ya kara da cewa bikin, wanda tarihinsa ya samo asali tun shekarar 1861 daga yankin Bula Wurbo, wata muhimmiyar gada ce ta al’adu da ke tallafa wa rayuwar al’umma da kuma karfafa tattalin arzikin yankin.
Gwamnan ya kuma yaba wa Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, bisa kokarinsa na farfado da bikin tare da sabunta shi domin samar da damammaki ga tattalin arziki da yawon bude ido.
Haka kuma ya bayyana cewa ya halarci bikin a madadin kungiyar gwamnonin Najeriya, inda ya jaddada aniyar su na ci gaba da tallafawa shirye-shiryen da ke bunkasa yawon bude ido da ci gaban al’umma.
Bikin ya samu halartar manyan baki, ciki har da wakilan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da na Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, da kuma Firayim Ministan Grenada, Dickon Mitchell.
Bikin Nwonyo na ci gaba da zama daya daga cikin manyan bukukuwan al’adu a Najeriya, wanda ke hada al’umma, kare al’adu, da kuma samar da hanyoyin bunkasa tattalin arziki ta hanyar yawon bude ido.
