Jumlar mutane sama da miliyon biyu ke dauke da cutar corona bairos a fadin duniya.
Wannan shine adadin yawan mutanen da ke dauke da cutar kamar yanda yake a shafin hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO da take wallafawa.
A yanzun dai mutane 2,013,918 aka samu suna dauke da cutar.
Cutar dai a waccan satin ne ta cika kwanaki dari da sanin asalin cutar.