Mutane 25 Sun Rasa Rayukansu Bayan Kifewar Kwale-kwale a Jigawa

Akalla mutane 25 ne suka rasa rayukansu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a ƙaramar hukumar Guri ta Jihar Jigawa, da ke arewacin Najeriya.

Sakataren ƙaramar hukumar Guri, Alhaji B. Jaji Adiyani, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa kwale-kwalen ya taso ne daga garin Adiyani da ke ƙaramar hukumar Guri, zuwa garin Garbi a ƙaramar hukumar Nguru ta Jihar Yobe.

A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, sakamakon lodi fiye da kima da aka yi wa kwale-kwalen.

“An ɗora wa kwale-kwalen mutane sama da 40, alhali adadin da ya kamata ya ɗauka bai kai hakan ba. Wannan sakaci ne da ya janyo kifewarsa,” in ji shi.

Alhaji B. Jaji Adiyani ya ƙara da cewa zuwa yanzu an zaƙulo gawar mutane 25 daga cikin ruwan.

“Daga cikin waɗanda suka mutu, mutane uku ’yan asalin Jihar Jigawa ne, yayin da sauran ’yan Jihar Yobe ne. An riga an kai gawarwakin zuwa jiharsu domin gudanar da jana’iza,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa jami’an ceto sun samu nasarar ceto mutane aƙalla 10 da ransu, waɗanda aka garzaya da su Babban Asibitin Nguru domin samun kulawar gaggawa.

A lokuta da dama, kifewar kwale-kwale na haddasa asarar rayuka a sassan Najeriya, lamarin da masana ke dangantawa da sakaci, lodi fiye da ƙa’ida, da rashin bin dokokin sufuri ta ruwa.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version