Me Ya Kamata Ku Sani Game da Sarauniyar Tsuntsaye – Mikiya

Babu wani abu da wannan tsuntsu yake sha’awa fiye da ya ci danyen nama. Ku saurari labarin domin jin yadda wannan tsuntsu mai ban mamaki yake rayuwa.

Mikiya ta farko an gano ta ne shekaru miliyan 36 da suka wuce a ƙasar Amurka ta Arewa, duk da cewa akwai ire-irenta a wasu sassan duniya.

Mikiya tana daga cikin tsuntsayen da babu abin da iska mai ƙarfi ko tsawa yake musu yayin ketare hazo. Sau da yawa ma idan suna jin nishadi tana iya tashi har ta wuce gajimare.

Masana sun ce mikiya ce tsuntsu mafi ƙarfi wajen farauta. A wasu lokuta, idan ta ga dama, har ɗan jaririn mutum ma tana iya ɗauka.

Wannan tsuntsu yana da idanu masu ƙarfi waɗanda karfinsu ya ninka na mutum sau 6 zuwa 8, tare da hangen da zai iya kaiwa kusan mile 2.

Mikiya na iya rike abincinta ko ya kai nauyin 2.5kg, ta kuma tashi da shi cikin sararin sama. Bakin ta kuwa na iya yage nama har ya kai nauyin 13 pounds a lokaci guda daga jikin abincinta.

Wannan tsuntsaye kan rayu cikin koshin lafiya ne saboda suna cin abincinsu baki ɗaya, sai dai kawai abubuwan da jikinsu ba zai iya amsawa ba su kan amayar da su.

Abin burgewa shi ne: mace a koyaushe ta fi namijin girma. Kuma abin mamaki, mikiya tana yin aure ne na har karshen rayuwarta.

Wannan tsuntsu kuma na iya yin gudu har 100 mph a cikin awa guda. Sun fi son yin sheƙansu a saman bishiyoyi masu tsayi a daji.

Rayuwar su kan kai shekaru 20 zuwa 30 a duniya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version