Ra’ayin Matashiya Tasneem Kabir akan Tsarin biyan harajin N100 da yan keke napep zasu biya a kano.

Matashiya Tasneem Kabir kuma daliba tace mutane suna cikin bakar wahala saboda rashin yan keke napep acikin awa 24 na yajin aikin su a kano

A zantawan mu da Matashinyar tace wannan ba tsari bane da za’a iya amfani dashi a Nigeria wanda za’a ce ko wanne Dan Sahu ya biya Naira 100 a banki ta hanyar internet tace kudin da za’ayi amfani da shi da lokacin da za’a bata to tabbas zai iya illah matukar gaske da mutane ta hanjar da zai sa ba zasu iya yin sana’ar Dan Sahu ba wanda su dama ba karfi suke da shi ba.

Da yawa daga cikin su basu suke da mallakar Keken ba karbowa suke su ringa bada balance.

Tace Gwamnati wajibi ne gare ta tanemo mafita mai sauki wurin da zai bawa yan sahu biyan wannan haraji ko da a hanu ne.

Duk wani dan Nigeria da yake amfani da kafar sadarwa na zamani yasan yadda ake shan baqar wahala da tsarin biyan kudi ta internet saboda babu isasshen hanyar sadarwa mai karfi da Zai basu damar biyan kudin kudin akan lokaci. Misali shine dalibai lokacin biyan kudin makaranta kowa yasan yadda suke shan baqar wahala wurin biyan kudi ta yanar gizo, toh ku lissafa irin wahalar da dan adaidaita zai shiga idan akace kullum sai yabi ta wannan hanyar

Tasneem Kabir.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version