By Hassan sani saidu
Garin Geidam na Jihar Yobe ya cika da murna da farin ciki a yau yayin da matashin ɗan siyasa kuma mai taimako ga al’umma, Idriss Yaro Gumsa, ya kaddamar da wani shirin tallafi na musamman da ya shafi marayu, dalibai da matasa.
Shirin, wanda ya ja hankalin shugabannin al’umma, malamai, iyaye da matasa, ya kunshi raba Naira miliyan 7 kai tsaye ga marayu da matasa marasa aikin yi domin su fara kananan sana’o’i da kuma koyon ɗabi’ar dogaro da kai. Gumsa ya bayyana cewa manufar tallafin shi ne rage wahala, karfafa tattalin arzikin gida da kuma kau da matasa daga fadawa cikin miyagun halaye.
Baya ga tallafin kuɗi, an kuma raba sabbin kekuna ga ɗalibai da dama domin rage musu wahalar yin nisan tafiya zuwa makaranta. Haka kuma, yara sun samu littattafan rubutu, alkaluma da sauran kayan karatu, abin da iyaye da malamai suka bayyana a matsayin taimako mai muhimmanci a wannan lokaci da tattalin arzikin kasa ke fama da tsada.
A cikin jawabinsa, Gumsa ya tabbatar da cewa wannan shiri ba shi ne na ƙarshe ba, yana mai cewa:
Wannan tallafi kashi ne na farko, akwai shirye-shiryen cigaba da kawo ayyuka a fannin ilimi, kiwon lafiya da koyon sana’o’i ga matasa da mata a Geidam da fadin Yobe.
Shugabannin al’umma da malamai sun yi ta jinjina ga wannan mataki, suna cewa tallafi irin wannan shi ne abin da ake bukata domin gina al’umma mai nagarta. Iyaye kuwa sun nuna godiyarsu da addu’o’in alheri, suna bayyana Gumsa a matsayin haske da fata ga sabon ƙarni na matasa.
Taron ya gudana cikin nishadi da murna, inda marayu, dalibai da matasa suka cika da farin ciki, suna jin cewa an tuna da su.
Masu sharhi kan harkokin siyasa sun bayyana cewa irin wannan tsari na Gumsa yana canza fuskokin siyasa a Yobe, domin ya haɗa siyasa da aiki na alheri ga al’umma kai tsaye.