Hafsat Yusuf, matar da ta haifi jarirai ’yan biyar a Asibitin Murtala Muhammad Specialist Hospital a ranar Laraba, ta rasu.
Mijinta, Salisu Nafiu, ne ya tabbatar da rasuwarta a safiyar ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa ta rasu ne a cikin asibitin da misalin ƙarfe 1:00 na dare.
Sai dai ya ce dukkan jariran guda biyar maza uku da mata biyu na raye kuma suna karɓar kulawar likitoci a asibitin.
Salisu Nafiu bai bayar da cikakken bayani kan musabbabin rasuwar matarsa ba, amma ya tabbatar da cewa likitoci na ci gaba da kula da lafiyar jariran domin tabbatar da suna cikin ƙoshin lafiya.
Tun da farko dai an ruwaito cewa Hafsat Yusuf ta haifi jariran ne ta hanyar tiyata (Caesarean section) da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Laraba a asibitin.
Mijinta, wanda ke sana’ar tuka adaidaita sahu, ya bayyana farin cikinsa kan nasarar haihuwar a lokacin, yana mai cewa wannan shi ne haihuwar matarsa ta tara.
Ya kuma bayyana cewa ma’aikatan lafiya a asibitin suna ba jariran kulawa ta musamman domin tabbatar da lafiyarsu da ci gabansu.
A wani bangare kuma, Gwamnatin Jihar Kano State ta sanar da cewa za ta dauki nauyin kula da lafiyar jariran gaba ɗaya.
Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta ce wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnati na karfafa kula da lafiyar mata masu juna biyu da jarirai, tare da rage mace-macen mata da kananan yara a lokacin haihuwa.
Karanta Gwamnan Kano Ya Sauke Sagagi Daga Mukamin Kwamishina
