Ƙungiyar Kwankwasiyya ta sanar da cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya miƙa murabus daga mukaminsa, a wani mataki da ta ce an ɗauka domin tabbatar da zaman lafiya da kuma bai wa ofishin damar gudanar da aikinsa cikin kwanciyar hankali.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed, ya fitar, ya bayyana cewa matakin murabus ɗin ya zo ne domin kauce wa duk wata tangarda da ka iya hana gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.
Sanarwar ta jaddada cewa murabus ɗin ba yana nufin Mataimakin Gwamnan ya amince da zarge-zargen da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi masa ba. A cewar sanarwar, Mataimakin Gwamnan ya tabbatar da cewa yana da tsabtataccen tarihi a harkokin gwamnati kuma bai aikata wani laifi ba.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin rage zafin rikicin siyasa da ka iya kawo tsaiko ga tafiyar gwamnatin jihar da kuma ci gaban Kano baki ɗaya.
Bugu da ƙari, sanarwar ta ce bayan murabus ɗin, Mataimakin Gwamnan zai mai da hankali wajen ƙarfafa ƙungiyar Kwankwasiyya da kuma tsara dabarun siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027.
A ƙarshe, ƙungiyar ta buƙaci magoya bayanta da al’ummar Jihar Kano da su kasance masu bin doka da oda, tare da ci gaba da goyon bayan shugabanci nagari domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.
