Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a Najeriya ta fara gudanar da babban taronta na kasa a birnin Abuja, inda dubban wakilai daga sassa daban-daban na kasar suka hallara.
An gudanar da taron ne a Eagle Square, inda wakilai sama da dubu takwas suka samu halarta, ciki har da gwamnoni, ‘yan majalisa da manyan shugabannin jam’iyyar.
Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan karfafa tsarin shugabanci na jam’iyyar, da kuma tattauna hanyoyin da za su taimaka wajen karfafa APC a zabuka masu zuwa.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da wasu manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar, ana sa ran za su halarci taron domin nuna goyon baya ga jam’iyyar.
An kuma tsaurara matakan tsaro a wurin taron domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da wannan muhimmin taro.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa sakamakon wannan taro zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar jam’iyyar APC a siyasance a Najeriya.
