Majalisar Dattawan Najeriya ta rage wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) lokacin da doka ta tanada na fitar da sanarwar zaɓe, daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 180 kafin gudanar da zaɓe.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewar majalisar da kudirin da Sanata Tahir Monguno ya gabatar, inda ya nemi a rage tsawon lokacin da ake buƙata kafin INEC ta fitar da sanarwar zaɓe.
Sanata Monguno ya bayyana cewa rage lokacin ya zama dole domin bai wa INEC damar bin tanadin doka cikin sauƙi, yana mai cewa idan aka bar kwanaki 360, hakan na iya jawo matsala ganin cewa lokaci ya riga ya ja dangane da babban zaɓen 2027.
Bayan wannan gyara, INEC za ta samu karin sassauci da isasshen lokaci wajen fitar da sanarwar shirye-shiryen zaɓen 2027.
