Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un. Allah Ya yi wa Hajiya Umma El-Rufai rasuwa, wadda ita ce mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Rahotanni sun bayyana cewa Hajiya Umma El-Rufai ta rasu ne a ‘yan sa’o’i da suka gabata, lamarin da ya jefa iyalai da makusanta cikin jimami.
A cikin wata sanarwa da iyalan suka fitar, sun bayyana cewa suna gode wa Allah bisa rayuwar da ta yi mai cike da tarbiyya da kyawawan dabi’u, tare da addu’ar Allah Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya kuma ba ta Aljannatul Firdaus. 🤲
Iyalin sun kuma bukaci al’umma da abokan arziki da su sanya marigayiyar cikin addu’o’insu, tare da rokon Allah Ya jiƙanta da rahama, Ya kuma ba iyalanta haƙurin jure wannan babban rashi. 🕊️
Allah Ya jikanta da rahama, Ya gafarta mata, Ya sanya Aljanna ta zama makomarta. Amin. 🤲
