LASTMA ta kwace motoci 27 a Legas

Hukumar Kula da Harkokin Zirga-zirga ta Jihar Legas (LASTMA) ta bayyana cewa jami’anta sun kwace motoci 27 bisa zargin karya dokokin tuki da ke barazana ga lafiyar masu amfani da hanya.

Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan yawaitar dora kaya fiye da kima a kan motoci, lamarin da ta bayyana a matsayin abin da ya zama ruwan dare kuma ke da matuƙar haɗari ga tsaro a kan hanya.

A cewar LASTMA, ta shafe lokaci tana wayar da kan direbobi tare da jan kunnen su ta hanyoyi daban-daban kafin ɗaukar matakin tsaurara dokoki.

Wata sanarwa da Daraktan Hulda da Wayar da Kai na hukumar, Adebayo Taofiq, ya fitar ranar Alhamis, ta bayyana cewa an gudanar da samamen ne da sassafe, inda jami’an suka kama motocin haya da na masu zaman kansu da aka samu suna saɓa ƙa’idojin ɗora kaya da dokokin tsaro.

Sanarwar ta kara da cewa an ɗauki matakin ne sakamakon ƙarin damuwa kan haɗarin da motocin da aka ɗora wa kaya fiye da kima ke haddasawa, musamman a manyan hanyoyi da kuma titunan cikin birni masu cunkoso.

Binciken da hukumar ta gudanar ya nuna wani yanayi mai tayar da hankali, inda direbobi musamman na motocin haya ke dora wa motoci kaya iri-iri ba tare da la’akari da lafiyar fasinjoji da sauran masu amfani da hanya ba.

Janar Manajan LASTMA, Olalekan Bakare-Oki, ya jaddada cewa irin wannan ɗora kaya ya saɓa dokokin zirga-zirgar ababen hawa na Jihar Legas, kuma yana jefa fasinjoji da sauran jama’a cikin babbar barazana.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version